Zaben Sanatan Yobe Zone B: Bomai, Gatan Al’umma

0
1039
Alhaji Ibrahim Bomai

Daga Hassan M. Yalwa Kafaje, Potiskum

A cikin al’umma, wadda ake samun masu tausayi da kishin al’ummar su, wannan al’umma bazata taba yin rashi ba ballantana tayi dana-sani. Haqiqa duniya takan yabawa mutane masu nagarta, wadanda suke taimaka wa al’ummar su, bawai wadanda suke da tarun dukiya ba. Kaza-lika, yabo yana tabbata ga wadda yayi aikin kwarai. Tabbas, a tarihin Jihar Yobe, mutane irinsu Alhaji Ibrahim Mohammed Bomoi baza’a taba mancewa dasu ba saboda qaunarsu ga al’umma.

Alhaji Ibrahim Mohammed Bomoi de an haifeshi a ranar 10 ga watan Fabreru alif 1960 a birnin Maiduguri. Yayi nasarar kammala karatunsa na matakin farko wato (primary) a makarantar Shehu Garbai dake birnin Maiduguri a alif 1972. A alif 1977 ne ya samu nasarar mallakar takardar shaidan kammala karatu mataki na biyu wato (secondary) daga makaranta mallakar gwamnatin tarayya dake Maiduguri. Saboda soyeyyar da yake yiwa neman ilimi, ya tafi mataki na gaba inda ya samu nasarar kammala karatun Diploma dama Digiri ta farko duka a Kaduna Polytechnic inda ya karbi shaidar karatu akan kimiyar lissafi na kudi (Accountancy) a alif 1982. A bisani, yasamu damar kammala yiwa qasa hidima wato (NYSC) a kolejin ilimi dake Ngsube a alif 1983. Kaza-lika, a alif 1997 ya samu nasarar kammala karatun Digiri ta biyu wato (Masters) a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi akan ilimin gudanar da kasuwanci.

A bisani, Ibrahim Bomoi ya fara aiki da Gwamnati a matsayin ofisa mai lura da harkar kudi a Cibiyar Bunqasa Harkar Noma wato (BOADAP) ta Jihar Borno a alif 1984, daga baya kuma ya riqe matsayin Babban Akawu (Senior Accountant) a kolejin tarayya (Ramat Polytechnic) dake Maiduguri a alif 1986. Tabbas hazaqa da kuma ilimi da Allah ya bashi, abun a yaba ne lura da irin muqame na gwamnati daban-daban daya riqe. Muqamen dasuka hada da mataimakin Babban Akawu (Assistant Chief Accountant), Ma’ajin kudi (Bursar) duk a kolejin ilimi, kimiya da fasaha dake garin Potiskum (FECT), Babban Akawu (Accountant General), dama Babban Mai Bincike (Auditor General) duk a ma’akatar tarayya wadda take lura da birnin Abuja.

Wannan haziqin, Ibrahim Bomoi yayi karatu a Makarantar koyar da shugabanci dake London, a bisani kuma aka nadashi amatsayin Daracktan Asusu na ma’aikatar dake lura da birnin Abuja daga alif 2008 zuwa 2016. Bomoi de be tsaya anan ba domin yayi aiki a matsayin Sakataren din-din-din a ma’aikatu daban-daban dake birnin tarayya Abuja. Abun farin ciki kuma shine, jarumin ya kasance daya daga cikin wadanda sukayi karatu a Cibiyoyin horo daban-daban wadanda sun hada da (Chartered Institute of Accountant,  the Association of National Accountants of Nigeria, Chartered Institute of Taxation of Nigeria, Chartered Institute of Treasury Management of Nigeria da Chartered Institute of Corporate Administrators of Nigeria). Be tsaya anan ba, ya karbi kyaututtuka  daban-daban na yabo daga gwamnatin tarayya saboda irin gudun-mawa daya bayar. Kyaututtukan sun hada da (National Productivity Merit Award, Distinguish Meritorious Award da kuma Outstanding Prowess of Administrative Matters Award).

Babu musu, qwarerren ma’aikacin ya taimaka wajen daukan dawainiyar kimanin matasa sama da dari domin suyi karatun Digiri nasu ta farko a cikin Nigeria harma da qasashen qetare. Domin inganta rayuwarsu, ya samarwa matasa kimanin sama da talatin aikin-yi. Tabbas, taimakonsa be tsaya anan ba domin ya kasance mai tona rijiyoyi na Boreholes domin samarwa al’umma ruwan-sha mai tsafta.

Haqiqa, mutane sunfi-sanin Ibrahim Bomoi da Mai-shinkafa saboda irin yadda yake taimakawa al’ummarsa dama maqobtan garurruwa musamman a lokacin azumin ramalana. Tabbas, halin qwarai irin nasa abun a yaba-ne.

A yanzu de, Dottijo mai halin kirkin-nan yayi qudurin neman takara domin ya wakilci al’ummar Yobe ta kudu a Majalisar Dottawa a qarqashin Jam’iyyar hadaka ta APC Mai-mulki. Kuma qudurin nasa yazo a lokacin da al’umma ke buqatar irinsa masu kishin al’ummarsu domin suma su amfana da romon demokiradiya. Allah ya bashi nasara domin ya tabbatarwa al’ummar dayake wakilta manufofinsa.

Daga qarshe de, daga zuwan jarumin, ya chanza salon siyasar Jihar ta Yobe yayinda ya baiwa matasa maza da mata damar taka-rawa da fada-aji a cikin tafiyar siyasar tasa. Tabbas nasarori da abubuwan alkhairi daya cimma abun farin ciki ne, kuma abun ayaba masane. Lokaci yayi da zamu fito qwai-da-qwarqwata domin mu zabi wadda ya chanchanta, me halin nagarta da kuma kishin al’ummar sa. Yakamata mu hada hannaye domin samar da wata al’umma wacce adalci da zaman lafiya zai mata jagoranci domin tanadar wa yara masu tasowa ingantaccen rayuwa dama kyakkyawan wakilci domin amfana da wakilci mai amfani a zauren Majalisar Dottawa. Zamu cimma hakane a lokacin da mukayi zabi nagari a zabukan Shugaban qasa, ‘Yan Majalisar Dottawa dama ‘yan Majalisar wakile na tarayya a zabe me zuwa cikin wani mako. Yanzu ne ya dace mu-zabi mai nagarta wadda zai cire mana kitse a wuta kuma ya wakilcemu na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Zaban mai nagarta, haqqinmu ne baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here