Yadda wasu masu garkuwa da mutane suka kashe wani yaro a Potiskum

0
1269
Marigayi Al'ameen, dan shekara biyar.

Daga Ibraheem El-Tafseer, Potiskum

Wasu mutane sun saci wani yaro mai suna Al’amin Adamu da ke zaune a garin Potiskum, Jihar Yobe har sun kasha shi bayan sun nemi mahaifinsa da ya ba su zunzurutun kudi har Naira Miliyan takwas a matsayin kudin fansa duk da daga bisani sun dawo har Naira 50,000. Sai dai sun shiga hannun hukuma lokacin da su ka je karbar kudin fansar.

Wani daga cikin ‘yan uwan yaron ya ce, “Al’amin Adamu ya fita da daddare da misalin Karfe 7:30 ne to sakamakon yara suna wasa a anguwar a lokacin hankalin mu bai kawo komai ba, bayan mun yi sallar Isha’i mun ci abinci sai labari ya riske mu akan ba a gan shi ba kuma an duba ko ina a cikin anguwar.

“A lokacin sai muka bari akan ko ya shiga wani waje ne ya kwanta dan haka ma hankalin mu bai tashi ba sakamakon haka inda muke cin abinci har lokacin watsewar mu yayi bamu gan shi ba. Sai mahaifinsa ya kira mu ya sanar da mu cewa har yanzu ba a gansa ba”.

Ya ci gaba da cewa “A wannan lokacin da yake muna da yawa wannan ya kira wannan, wancan ya kira wancan a waya ya shaida masa abinda yake faruwa sai muka hadu muka shiga cikin gari domin neman sa, duk inda muka sani a cikin garin Potiskum sai da muka shiga neman sa amma bamu same shi ba. Har muka sa mota ta mana cikiya amma ina ba’a same shi ba.

“Washe gari ranar Alhamis da daddare bayan mahaifin yaron ya shiga gida sai yaga an aiko wani yaro dauke da takarda a hannun sa an rubuta cewa maman Haidar ta kira wannan lambar. Sai suka fito da yaron da nufin su je wajen mutumin da ya aiko sakon koda suka zo wajen babu kowa,bayan ya dawo gida sai ya kira wannan lambar, sai yaji ance masa dan ka ba bata yayi ba yana nan a raye munyi garkuwa (Kidnapping) da shi ne.

“Sai suka ce suna neman kudin fansa Naira Miliyan Takwas, kafin su saki yaron mahaifin yaron yace gaskiya bazai iya bada wannan kudin ba amma ya nemi su sanya masa muryar yaron ya ji sannan sai aci gaba da magana. Ana ta haka dai amma sai suka ki aminta da ayi magana da yaron, aka ci gaba da magana akan kudin har suka dawo Miliyan biyu kuma daman tun daga farko ya fada mana cewa shi daga Zamfara ya ke an turo shine mussaman domin yin wannan aikin.

“Bayan kwana biyu ya sake kiran waya yana fadin cewa a tura masa kati zai kira mai gidan sa suyi magana, to da ikon Allah dai ana ta bincike kuma ana addu’a, sai yace aje Tandari (wata anguwa ce) cikin masallacin juma’a a ajiye masa Naira dubu 50. Bayan mun kai kudin sai shima kansa bai yarda da wajen ba sai ya ce ya chanza wajen kudin.

“Sai yace da daddare ya dawo anguwar su layin makarantar Malam Mai Buzu da misalin karfe 2:00 ya ajjiye kudin, to bayan ya zo ne sai ya gansa tare da wani mutumi a tsaye dan haka sai yaki fitowa daga inda yake, kuma lokacin daman mun sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki kuma sun bibiyi lamarin.

“Ya ki yarda a hadu da shi a karbi kudin sai yace a je Gadar Sokal a jefa kudin ciki, a lokacin sai mu kayi shawara kuma muka kara kiran yan sanda muka fada musu halin da ake ciki suka zo muka tafi da su tare da DSS a cikin mota, bayan mun isa wajen sai muka yi abinda suka umarce mu da yi, muka jefa muka bar wajen ya kira mu ya fada mana mu bar wajen ya dauki kudin.

Baban Al’ameen

“Mun bar wajen duk da yake bamu aminta da cewa ya dauki kudin ba tunda akwai jami’an tsaro a wajen, nan ma ya kira mu a waya kan cewa mu koma dogon karfe zasu fito mana da yaron a cikin wata jar mota, to a lokacin ya kwadaitamu da hakan sabida muna son ganin yaron sai muka tafi zuwa wajen.

“Mu ka zo wajen muna jira muga yaro har wajen misalin karfe goma na dare babu alamar sa bamu ga kowa ba sai ga kiran wayar jami’an tsaro kan cewa sun damke su daga nan muka zo dasu ofishin ‘yan sanda aka fara gudanar da bincike bayan an gama binciken ne aka tura su zuwa ofishin DSS dake Damaturu babban birnin jihar Yobe.

“Ana ta bincike dai sai ya ke nuna shi bai san inda yaron ya ke ba, har yake fadin wayar ma ba tasa bace karba yayi daga wajen wani wais hi Adamu mu kuwa muna ta addu’a muna zaune dai a gida sannan muka kama hanyar zuwa Damaturu muka same shi da yan’uwan sa suna ta rokon shi ya fadi inda ya kai yaron shi kuma yace bai san inda yaron ya ke ba.

Maman Al’ameen.

“Bayan wani lokaci sai yace zai fada, ya ce lokacin da aka dauko yaron an jefa shi a cikin wani rami kuma zai iya gane ramin. Aka tambaye shi ko ya san yaron? Sai ya ce shi bai san ko dan waye bane amma dai ya zo anguwar yaji ana cikiya. Daga nan muka dauko shi a cikin mota muka zo ofishin ‘yan sanda suka hada mu da wata mota muka wuce wajen da suka saka yaron.

“Mu ka samu muka bude ramin domin bayan sun jefa shi a ramin sun rufe muka sami ramin an jefa yaron a ciki kuma an fasa kirjin shi gashi kuma an cire wasu sassa na jikin sa kamar irin su makogoro, idanuwa da kuma gabansa. Dan haka mu a lissafin mu tun lokacin da suka dauki yaron suka kashe shi, a takaice wannan ba garkuwa bane kisa ne.

Ramin da aka sami gawar Al’ameen.

“Muka ciro shi sakamakon bazai yiwu a masa wanka ba haka dai muka wuce da shi zuwa makabartar bayan asibitin Misau Road muka bizne shi.

Gawar Al’ameen.


“Koda wakilin mu ya tambaye shi ko akwai wasu mutane da ake zargi cikin wannan lamarin? Ya amsa masa da cewa, zuwa yanzu bazai iya cewa komai ba, amma kuma hukuma tana bincike a kan hakan. Shugaban rundunar ‘yan sandan Potiskum, DPO Baba Kura Mustafa, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ‘muna nan ana gudanar da bincike akan wadanda aka kama, kuma daga lokacin da aka kammala za a dauki matakin da ya dace da su.”

Wadanda aka kama da zargin kashe Al’ameen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here