Wani matashi ya cakawa kansa wuka a Potiskum

0
420
Umar Mande

Daga Ibraheem El-Tafseer, Potiskun

Wani matashi mai suna Umar Mande, mai kimanin shekaru 35, ya cakawa kansa wuka a garin Potiskum ta jihar Yobe. Amma cikin ikon Allah bai mutu ba.

Yadda al’amarin ya faru kuwa shine, shi dai wannan matashi, shi da abokanansa suna shaye shayen su a wata mashaya da ake kira Dorawa a cikin garin Potiskum, sai rikici ya hada su akan giyar Wiski, wadda takai ga har shi Umar Mande ransa ya baci, saboda ba a bashi ya sha ba.

To wannan bacin ran ne yasa ya cakawa kansa wuka a cikin sa, inda nan take ya fadi, aka dauko shi cikin gaggawa zuwa babban asibitin Potiskum. Yanzu haka dai likitoci suna kokarin ceto rayuwarsa, sannan kuma jami’an ‘yan sanda, suna binciken lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here