Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Yobe ya Sauya Sheqa Zuwa Jam’iyyar APC

0
757
Sani Inuwa Nguru a daman Shugaba Buhari.

Daga Hassan Yelwa Kafaje, Damaturu

Qasa da awanni arba’in kenan da zaben Shugaban qasa da ‘Yan Majalisun Dottawa dana wakile a ranar asabar, Shugaban jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Yobe, ya chanza sheqa daga Jam’iyyar tasa zuwa Jam’iyyar hadaka ta APC mai-mulki.

Shugaban, Alhaji Sani Inuwa Nguru a yau dinnan ne yaje gidan gwamnatin tarayya dake Abuja domin nuna goyon bayansa ga shugaba Buhari. Haka kuma ka iya janyowa Jam’iyyar PDP naqasu yayinda za’aje runfuna zabe bata da Shugaba. Kuma anasa rai, shugaba Buhari zai iya kada abokin hamayyarsa, Aitku Abubakar a jahohin Arewa naso gabas, wato Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Jihar Yobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here