Onorabul Mai Mala Buni Ya Lashe Zaben Gwamna A Yobe

0
1163
Onorabul Mai Mala Buni.

Daga Hassan Yelwa Kafaje, Damaturu

Hukumar INEC ta tabbatar da Onorabul Mai Mala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Yobe inda ya doke abokin hamayyarsa, Ambassador Umar Bello Iliya na jam’iyyar PDP.

Onorabul Mala Buni ya samu jimillar kuri’u 444,013 yayin da Ambassador Iliya ke da kuri’u 95,703 daga jimilar kuri’u 560,492 da aka kada.

Wannan ne zabe na farko a jihar Yobe da jam’iyar da tazo na biyi ta gagara cin ko da akwati daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here