Me yasa gwamnatin jihar Yobe ta garkame Bulama Lamba?

1
1394

Daga Adamu Ngulde, Damaturu

Rahotanni daga garin Potiskum na jihar Yobe na cewa gwamnatin jihar ta garkame Mallam Bulama Lamba a gidan yari sakamakon ya bayyana ra’ayinsa a shafinsa na Facebook.

Neptune Hausa ta nemi jin ta bakin makusantan Bulama Lamba amma
hakkarmu ta citura sai dai Muhammad Suleiman, wanda kani ne ga Bulama Lamba ya bayyanawa Muryar Amurka cewa ”Gwamnatin jihar Yobe ta cafke yayanmu ne sakamakon ya yi rubutun cewa karramawar da aka yi wa Gwamna Ibrahim Geidam na cewa shi ne wanda ya fi kowa biyan ma’aikata kudin fansho ba gaskiya ba ne, idan hakane a matakin jiha ake biya ba a kananan hukumomi ba domin kuwa akwai ‘dan uwanmu marigayi ya rasu tsawon shekara shida har zuwa yanzun ba a biya ko kobo ba kuma ire-irensa sunanan dayawa wannan shi ne abinda yasa aka tsareshi a gidan yari”.

Shi kuwa kwamishinan ‘yan sandan jiyar Yobe Abdulmalik Sumono ya ce
”Ana tuhumarsa ne a karkashin dokar laifuka na yanar gizo sashi na 24 da kuma na 25 na shekara ta 2015 kuma a halin yanzu gwamnatin jihar ta karbi batun daga hannunmu”.

Sanin kowane dai gwamnatin jihar na muzgunawa al’ummar jihar mussamman wadanda suke bayyana ra’ayoyinsu a shafukan jaridu ko kafafen yad’a labarai.

Anasa mahangar, masanin harkokin shari’a lauya Hassan Liman ya bayyana cewa ”Kowane dan Najeriya ma’aikaci ne ko kuwa dan kasa yana da damar fadin ra’ayinsa wanda ya ga dacewar hakan ba tare da kage ba”.

Lauyan ya ci gaba da cewa ”A kashi na 24 zuwa 25 kowane dan kasa zai
iya bayyana ra’ayinsa matukar babu kage ciki har ila yau a karkashin
kashi na 39 ya baiwa kowa dama mussamman dan Najeriya da ya fadi
ra’ayinsa’.

”Kana sai an tabbatar da cewa abinda Bulama Lamba ya rubuta ya ci karo da doka ko batawa gwamnati suna kafin a tuhumeshi da laifi.”
Amma matukar ba a sameshi da laifi ba to babu yadda za a tuhumeshi da
laifin batawa gwamna suna a karkashin kashi 39 na dokar laifuffuka na Final Kot na Najeriya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here