Mayakan Boko Haram sun kai hari a kauyuka biyu a jihar Adamawa

0
550

Daga Usman Bin-affan, Damaturu

Kungiyar Boko Haram ta sake kai hari a wasu kauyuka biyu dake yankin Madagali a jihar Adamawa inda, kamar yadda suka yi makon jiya suka kone gidaje da abinci da dabbobi kurmus.

Kamar yadda rahotanni ke cewa, mayakan na Boko Haram sun kai harin ne a Muduhu da Nyibango tare da kona gidajen mutane da abinci, wanda kawo yanzu babu cikakken alkalumman wadanda lamarin ya shafa.

Wani da ya tsallake rijiya da baya yace mayakan Boko-Haram din sun yi shigar burtu ne tamkar ‘yan banga cikin dare wanda nan take sai suka soma harbi ba kakkautawa da kuma kone kone.

Hukumomin tsaro dai a jihar Adamawa basu ce komi ba kawo yanzu, to sai dai kuma shugaban karamar hukumar Madagalin,
Yusuf Muhammad ya tabbatar da wannan sabon hari inda yace abun takaici ne abubuwan dake faruwa a baya-bayan nan na hare-hare.

Kamar dai shugaban karamar hukumar, shima dan majalisar wakilai dake wakiltar yankin Michika da Madagalin, Mr Adamu Kamale ya tabbatar da aukuwan lamarin inda ma ya musanta batun cewa babu sauran ‘yan Boko Haram a wadannan yankunan na Michika da Madagali da aka kwato dake kusa da dajin Sambisa.

Wata matsalar da ake fama da ita ma yanzu ita ce na yadda jami’an sojin dake aiki a wajen ba sa karkashin rundunan soji ta 23 dake Yola ko na Mubi, wato suna karkashin na Chibok dake jihar Borno, da hakan kan zama kandagarki ga jami’an gwamnatin jihar kamar yadda shugaban karamar hukumar Madagalin ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here