Maimuna Waziri: Mace ta biyu da ta zama Farfesa daga Yobe

0
816
Farfesa Maimuna Waziri

Daga Mahdi Garba, Gashua

Ilimin ‘ya mace a arewacin Nijeriya wani abu ne da ba a cika ba shi muhimmanci ba, a wannan yanayin ne Farfesa Maimuna Waziri ta samu nasarar zama mace Farfesa ta biyu a jihar Yobe.

An haifeta a shekarar 1966 a garin Gashuwa dake karamar hukumar Bade. Ta fara karantarwa ne a Jami’ar Maiduguri a matsayin mataimakiyar Malama a shekarar 1987 bayan ta kammala Digirinta na farko a Jami’ar Bayero dake Kano inda ta karanci sashen Sinidirai.  

Saboda tsayuwarta da jajircewarta wanda ya sa ta tsaya kyam a tsakanin sauran mata, Maimuna ta ci gaba da karatun digirinta na biyu a wannan sashen a Jami’ar Ibadan inda ta kammala a shekarar 1990. Sannan ta yi digirin-digirgir dinta a bangaren nazarin sinadirai a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2006.

Sha’awarta ga koyarwa yasa ta ci gaba da karantarwa a sashen nazarin Sinadarai na Jami’ar Maiduguri a matsayin babbar Malama.

Duk da kasancewarta Malama ce a bangaren nazarin Sinadarai, hakan bai hana Maimuna a shekarar 1997 ta zama Kwamishinar harkokin mata da ci gaban zamantakewa daga bisani ta zama Kwamishinar kasuwanci da harkokin ma’aikatu daga shekarar 1998 zuwa 1999.  

Har wala yau ta zama mataimakiya ta musamman ga Gwamna akan harkokin ci gaban ayyuka daga shekarar 1999 zuwa 2001. Sannan ta zama Daraktan Kimiyyah da fasaha, a ma’aikatar Hukumar ilimi dake Damaturu, daga shekarar 2001 zuwa 2007.

Farfesa Waziri tana daga cikin wadanda aka baiwa hakkin samar da Jami’ar Jihar Yobe, bayan an samar da Jami’ar a shekarar 2007, ta karantar a matsayin babbar Malama a sashen nazarin Sinadarai, a lokaci guda kuma ta zama Daraktan a makarantar Sharar fagen Shiga Jami’a, sannan ta zama Shugabar Tsangayar Kimiyya da fasaha daga 2007 zuwa 2009.  

Ta karbi kyaututtukan girmamawa daban-daban wanda suka hada da; kyautar tunawa da Michael Collins ta Sashen Sinadarai a shekarar 1984, sannan da kyautar wanda ya fi kwazo ta tunawa da Michael Collins a sashen Sinadarai a Jami’ar Bayero dake Kano a shekarar 1986. Da kyautar ‘Who is Who’ a bangaren sashen Ilimin kimiyya da fasaha ta Afrika, da sauran wasu kyaututtuka daban-daban.

Maimuna memba ce a kungiyar nazarin Sinadarai ta Nijeriya da wasu kwararrun kungiyoyi wanda suka hada da Cibiyar kwararru ta ‘Chartered Chemist’ ta Nijeriya, sai wata cibiyar mata kwararru ta binciken kimiyya da fasaha ta hadin guiwa ta duniya da kasashen masu tasowa.  

Ta sadaukar da rayuwarta gaba daya wajen neman Ilimi da bincike da karantarwa, sannan ta yi aiki a wurare daban-daban wanda suka hada da Jami’ar Maiduguri da Jami’ar Bukar Abba Ibrahim dake jihar Yobe (Jami’ar Jihar Yobe a yanzu) dake garin Damaturu, daga nan ta koma Jami’ar Tarayya dake garin Gashuwa inda aka kara mata girma zuwa matsayin Farfesa daga ranar 1 ga watan Oktoban 2015.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here