Maiduguri: Mutane da dama sun mutu a hare-haren kunar bakin wake

0
537

Akalla mutane 13 suka mutu yayin da wasu 65 kuma suka jikkata a harin da aka kai ranar Laraba.

Wasu ‘yan kunar bakin wake hudu ne suka kai harin a wajen birnin Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu majiyoyin tsaro sun ce hare-haren na kunar bakin wake ne da aka kai tashar motar Muna da ke kan hanyar Mafa-Dikwa, a garin Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

An bayyana harin a matsayin mafi muni a jerin hare-haren da aka kai a cikin ‘yan kwanakin nan a jihar Borno da ke fama da matsalar Boko Haram.

An dai sha kai hare-hare a tashar motar ta Muna, da ke kusa da sansanin ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

Hare-haren dai na zuwa ne duk da ikirarin da rundunar sojojin Najeriya ke yi cewa tana samun nasara a yaki da Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here