Magoya Bayan Marigayi Usman Albishir Kimani 200,000 Sun Goyawa Mai Mala Buni Baya

0
508
Hon. Mala Buni

Daga Hassan Yalwa Kafaje

Dan takarar Gwamna na Jam’iyyar hadaka ta APC, Mai Mala Buni ya samu nasarar karbuwa a wurin kimanin dubu-dari biyu na  magoya bayan dan takarar Gwamnan Jihar Yobe a Jam’iyyar PDP marigayi, Usman Albishir a garin Nguru dake Jihar ta Yobe.

A jiyane dan takarar Gwamnan Jihar Yobe na Jam’iyyar hadaka ta APC, Mala Buni ya samu karbuwa wajen dubban al’umma a garin Nguru wadanda a baya magoya bayan dan takarar Gwamnan Jihar ce a Jam’iyya PDP, wato Marigayi Albishir. Al’ummar sun tabbatar da hakane a jiya lokacin suka bayyana qudurinsu na chanza sheqa daga Jam’iyyar ta PDP zuwa Jam’iyyar hadaka mai-ci ta APC yayin da ake karbansu a garin Nguru.

Taron daya gudana de na daga cikin manyan taruka a tarihin siyasar Jihar Yobe wadda yasamu halattar kimanin mutane  dubu-dari biyu wadda ya hada da manyan ‘yan siyasa da magoya bayan Albishir.

Sanmun labarin hakan ne yasa dan takarar Gwamnan Jihar Yobe na Jam’iyyar hadaka ta APC yasamu rakiyar  Mai girma Gwamnan Jihar Yobe mai-ci, Alhaji Ibrahim Geidam, babban daraktan kamfen na Jam’iyyar, Alhaji Lawan Shetima, shugaban shiya na gudanarwa na Jam’iyyar, Alhaji Jinjiri Abubakar dama wassu manyan ‘yan siyasa a jiya alhamis zuwa garin Nguru.

Alhaji Abdullahi Balarabe Nguru wadda akafi-sani da Balarabe DJ, shugaba na tafiyar Albishir kuma Dan kasuwa mai taimakon al’umma shine ya jagoranci wadanda suka chanza sheqa zuwa Jam’iyyar hadaka ta APC wadda dan takarar Gwamnan ya karbesu a jiya alhamis a garin Nguru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here