Maganin basir ya kashe wani matashi a garin Potiskum

Mai rahoto: Yahaya Wakili, Potiskum

2
1567
Àdamu Jibirin

Wani matashi mai suna Àdamu Jibirin mai shekaru 28 da haifuwa dake layin Mosko a Potiskum, jihar Yobe ya rasa ransa a sanadiyar shan maganin gargajiya da wani mutum yabashi.

Kamar yadda kawunsa mai suna Alhaji Isa Mustapha ya baiyanawa Neptune Hausa, a ranar asabar data gabata ne Adamu Jibirin yasha maganin kuma daga sha sai amai da gudawa ba kakkautawa.

Alhaji Isa Mustapha ya cigaba dacewa sunyi iya kokarinsu domin su tsayar da wannan amai da gudawa amma abin yaci tura, shine yau (11/07/2017) talata da safe suka kaishi asibiti daga nan sai likita yayi masa allura ya kuma bashi magunguna yace su koma dashi gida amma bayan sun dawo gida sai yace ga garinku.

Alhaji Mustapha ya baiyana cewa sunyi ta kiran wayan mai maganin amma yaki ya dauki wayan, ya kara da cewa zasu ci gaba da nemansa sai sun sameshi. Marigayi Adamu Jibirin ya rasu ya bar matarsa wacce watan su biyar da yin aure.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here