LABARAI: Gwamnoni shida sun taso don ganin bayan kungiyar Boko Haram

0
387
Gwamnan Yobe, Onorabul Mala Buni (hagu), Gwamnan Borno, Professor Zulum (dama).
Daga HARUNA HASSAN, Abuja

A wani yunkurin nemo mafita da madogara dangane da sha’anin matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya, gwamnoni shida da Babban Safeto Janar na yan-sanda, manyan jami’an tsaro tare da sarakunan gargajiya da malamai da shugabanin al’umma ne suka gudanar da babban taron tattauna matsalolin tsaro a Maidugurin jihar Borno.

Daga cikin manyan bakin da suka samu damar halartar babban taron tattaunawa akan batutuwan tsaron, akwai shugaban rundunar yan-sandan Nijeriya, Mohammed Adamu da Gwamnan jihar Yobe, Onorabul Mai Mala Buni da mataimakan gwamnonin jihohin Adamawa da Borno da Bauchi da kuma Gombe, tare da sauran manyan baki, a karkashin jagorancin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum. A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Borno ta fitar, ta bayyana tsara gudanar da babban taron tattauna muhimman lamurran tsaron, a babban dakin taron gidan gwamnatin jihar ‘Multi-Purpose Hall’ da ke Maiduguri, domin a hada karfi da karfe tare da lalubo ingantattun matakan dafawa wajen kawo karshen matsalar tsaron Boko Haram wadda ta addabi yankin, yau kimanin shekaru goma da suka gabata.

Bugu da kari kuma, baya ga gudanar da taron a gaban babban safeto Janar na yan-sanda, akwai kwamishinan yan-sandan jihar Borno, hadi da kwamishinan yada labarai na jihar Borno, Bakura Abba Jatto.

A hannu guda kuma, daga cikin mahalarta taron akwai yan majalisar tarayya da ke wakiltar jihar Borno, kwamandan rundunar Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi, jakadun jamhuriyar Chadi da Nijar da sarakunan gargajiya daga jihohin arewa maso gabas da yan boko tare da kwararru daga sassa daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here