Honorabul Mai Mala Buni Ya Samu Goyon Bayan Al’ummar Garin Fika Da Na Gadaka

0
832
Hon. Mai Mala tare da mataimakin sa, Alhaji Idi Barde Gubana.

Daga Comrade Haruna Sardauna, Damaturu

A cigaba da yakin neman zaben jam’iyyar APC SAK, a jiya Talata 5/3/2019 tawagar kwamitin yakin neman zabe karkashin da dan takarar gwamnan su, Hon. Mai Mala Buni, sun kaddamar da yakin neman zabe a Fika gari da Gadaka.

Taron ya samu halartar jiga-jigan yan siyasar dake kudancin jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya nemi goyon bayan al’ummar Fika gari da Gadaka, su zabe shi da ‘yan majilisu biyu dake mazabun gabashi da yammacin karamar hukumar Fika.

Hon. Mai Mala ya fara da godiya a madadin shugaban kasa da jam’iyyar APC, bisa irin ruwan kuri’u da talakawan Fika suka bayar wajen zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan Majalisar dattijai da wakilai na karkashin jam’iyyar APC.

Ya kuma saurari koke-koken al’ummar yankunan biyu wanda yakilan siyasar suka bayyana a jawaben su, sai sakon godiyar da suka bashi domin ya isar wa Gwamna Ibrahim Gaidam, Mai Mala yayi alwashin zai tabbatar gwamnatin sa tayi aiyukan, kuma zai isar da sakon godiya da suka aika shi zuwa Gwamna Ibrahim Gaidam.

Al’ummar Fika sunyi godiya a Gwamna Ibrahim Gaidam ne saboda hanya da ya yi musu na Gadaka, da kuma titi nakan hanya daga Godeli zuwa Siminti, da  gyara musu makaranta da mahimman aiyukan da gwamnatin shi tayi a karamar hukumar Fika bangaren noman rani, lafiya da dai sauran abubuwan more rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here