Hajiya Zulai Daya da Hajiya Hadiza Lavers: Mata na farko da suka fara kammala digirinsu a Yobe

0
944

Fassara daga Hussaini Mohammed Baba, Potiskum

Hajiya Zulai Daya

Hajiya Zulai Daya

Ita Malama ce wadda ta kafa tarihi na zama mace na farko da ta gama degree nata daga jahar Yobe (inda suka hada wannan darajar  da Hajiya Hadiza Lavers). Hajiya Zulai an haifeta ran daya ga watan Janairu na alif dubu daya da dari tara da arba’in da biyar a garin Daya dake karamar hukumar Fika a jahar Yobe.
Ta fara karatunta a Junior Primary School daga 1951 zuwa 1953, saita garzaya zuwa Provincial Girls School, Maiduguri daga 1954 zuwa 1959 kafin ta wuce ta samo shaidarta na grade 3 a Women Teachers College duka a cikin Maiduguri daga 1961 zuwa 1963. Ta samo takardar shaidanta ta Grade 2 a tsakanin 1965 da 1967 duk dai anan Maiduguri Women Teachers College.
Hajiya Hadiza Zulai Daya ta samu digirinta ne a harshen Turanci na Abdullahi Bayero College, inda akafi saninsa a yanzu da Bayero University Kano (BUK)  a shekara ta 1972, bayan ta samu shiga makarantar a 1967.
Ita ta zama mace na farko a Yobe inda ta samu shaidan wadda ta chanchanta ta fara koyarwa. Wadannan sune kadan daga cikin takai-taccen tarihinta na ayyukan da tayi:
(1) Ta koyar a Damboa Primary School 1962-1964
(2) Ta koyar a Godowoli Primary School (Na wata uku) 1965
(3) Ta koyar a Senior Primary School Potiskum 1966-1967
(4) Ta zama Shugaban Makarantan Kara Primary School Potiskum 1966-1967
(5) Ta koyar a Yerwa Government Day Secondary School Maiduguri 1972-1973
(6) Ta koyar a Government Girls College Maiduguri 1973-1978
(7) Ta zama mataimakin shugaban makaranta a Government Girls College Maiduguri da Teachers College Maiduguri a 1978-1979
(8) Majagaban babban makaranta na Government Girls Secondary School Miringa-Biu 1979
(9) Babban makarantan Women Teachers College Nguru a 1979-1980
(10) Hedkwatan hidiman ilimi dake Maiduguri 1980-1984
(11) Babban Makaranta na Government Girls College Maiduguri 1984-1985
(12) Shugaban makarantan Federal Government Girls College Potiskum 1985-2001
(13) Sufeto na gudanar da aiki na bangaren ilimi daga 2001-2005
Hajiya Zulai Abdullahi Daya, mace ta farko data fita daga cikin kauyen Daya dan neman sani, tayi retire a shekaran 2005 sannan tana rike da mukamin gargajiya na Magaram din Daya. Allah Ya bata ‘ya’ya biyar.

Hadiza Bomai Lavers

Hajiya Hadiza Lavers

Wata mata ta biyu wadda ta gama karatunta shekara daya da Hajiya Zulai itace Hadiza Bomai Lavers (‘Yar Ciroma). An haifeta ranar sha biyar ga watan Yuni na alif dubu daya da dari tara da arba’in da hudu a garin Potiskum, jahar Yobe. Taje Central Primary School daga 1952 zuwa 1953 inda daga nan ta wuce zuwa Provincial Girls School Maiduguri daga 1954 zuwa 1958 inda ta samu takardar shaidan ta na gama makarantanta na zagayen farko wato Primary School.
Hadiza Bomai ta tafi Post Primary Girls School a Kano a tsakanin January 1959 zuwa December na shekaran, daganan ta dawo Women Teachers College, Maiduguri a January 1960 zuwa December 1962 inda daga karshe ta samu takardan shaidan gama grade 3 nata.
Amma a sabaninta da Hajiya Zulai, Hajiya Hadiza ta samu takardan shaidanta na gama grade 2 a Women Teachers College dake Kano inda ta samu tayi nazari a January 1965 har zuwa December 1966.
Ta samu ta shiga Abdullahi Bayero College inda akafi sani da Bayero University Kano (BUK) yanzu, a October 1967, ta sami digirinta ita ma a harshen Turanci ne a June 1972.
Itace mace ta farko a Yobe data fara zama shugaban firamare.

Lura da kwarewan ayyukanta kamar haka :
-Malama a Potiskum
-Shugaban Race Course Primary School Potiskum 1963-1964
-Tutor Women Teachers College Kano daga June 1972 zuwa September 1972
-Shugaban Makarantan Primary dake cikin Bayero University Kano 1974-1981
-Member Yobe State executive council April 1996-1997 ( komishina na Matasa da Wasanni)

Kungiyoyin da tayi aiki dasu
(1) Borno State Scholarship Board Member 1975-1982
(2) Cubit Nigeria Limited -Director 1984
(3) Ramat Polytechnic Council -Member  daga January 1987 zuwa March 1989
(4) Borno State Hotels and tourism – Chairman daga  March 1987 zuwa July 1989
(5) Borno Express -Member  1989-1990
(6) Borno Radio and Television – Member  1991-1992
(7) College of Education Gashua -Chairman 1994-1995
Hajiya Hadiza wanda ayyukan futunta suke kamar haka: Lambu, Karatu, Dafa Abinci,  ta auri wanda takeso, Malama Lavers (Akan kirata Bomoi Bogaru) tayi aure, tanada yara guda hudu.
SHARHI
Wadannan mata guda biyu sun bada gudummawarsu wajen ci gaban ilimi a jihar arewa maso gabancin kasannan baki daya inda yanzu sune:Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, da kuma Yobe. Dukansu sunyi rawan gani kuma abin kwatance ne ga karatun yara mata kuma ya zama kalubalai ga yara maza dasu tashi suyi kwazo suyi abunda zai taimakesu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here