FAO Ta Tallafawa Manoma ‘Yan Gudun Hijira 141, 000

0
288

Daga Muhammad al-Amin, Damaturu

Qunyar farfado da ayyukan noma da samar da abinci, wadda aka fi sani da Food and Agriculture Organization(FAO)-qarqashin muqaddashin shugaban ta a Nijeriya, wato Mr Nourou Macki-Tall, ta qaddamar da raba kayan noma tallafi ga manoma dake sansanin yan gudun hijira a Shagari

Low Cost dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno, yayin da kimanin mutum 1,500 suka ci gajiyar sa.
Al’ummar wadanda yan asalin qwaryar Maiduguri da yankin Jere ne, sun amfana da tallafin nagartattun iraruwa da suka qunshi wake, masara, gero, dawa, takin zamani da makamantan su.

Yayin da kuma, sama da mutum 500 daga qaramar hukumar Jere suka ci gajiyar makamancin wannan tallafin.

Macki-Tall ya bayyana cewar hukumar su ta FAO ta tallafawa yan gudun hijira sama da 141,000 wadanda suka fito daga yankin arewa maso-gabas da kayan noma, a wannan shekara ta 2017.

Har wala yau, ya sake nanata cewa, FAO tana tafiyar da ayyukan ta ne tare da hadin gwiwar qungiyar bunqasa abinci ta duniya (WFP), da hukumar kula da jin dadin jama’a sannan kuma da ma’aikatar ayyukan gona ta jihar Borno, a daya barin.

Bisa ga wannan ne ma, babban daraktan hukuma mai kula da jin dadin jama’a na qasa, Mr Olisa Eloka,

ya tofa albarkacin bakin sa da cewa”baya ga wannan, akwai qarin wasu manoma 900 wadanda suka koma muhallinsu suka ci moriyar wannan shirin, a garuruwa da suka hada da Pulka da Gwoza tare da Izge. Sannan kuma, manoma daga birnin Maiduguri Metropolitan 1,100 ne suka samuwannan tallafin, a yankunan Shagari da a unguwannin Musari A da B. Yayin da a wasu yankunan mun karkata tallafin ne zuwa ga mata”, inji shi.

Shirin wanda ya qunshi baiwa manoma 67,000 da zasu ci gajiyar sa a jihar Borno, yayin da a

Yobe kuma manoma 41,000 ne zasu amfana inda mutum 32,000 a Adamawa zasu ci gajiyar sa. Haka zalika kuma, a qarqashin wannan tsarin nashekarar 2017 a Nijeriya hukumar FAO ta quduri aniyar kashe dala miliyan 62 wajen tallafawa mutane miliyan daya da digo tara ($1.9).

Ta bakin muqaddashin shugaban wannan hukuma a Nijeriya ya bayyana cewa “kawowa yanzu FAO ta cefanar da dala miliyan 17.5 a bangarori da dama na ayyukan noma inda sama da manoma miliyan daya da digo daya (1.1) dake yankin arewa maso-gabas wadanda rikicin Boko Haram suka kora daga muhallan su a Borno da Yobe da Adamawa suka ci alfanunsa.

Sannan bisa cigaban shirin, ko a cikin watan June manoma maza da mata kimanin 1,000, wadanda suka fito daga Benisheik ta jihar Borno sun karbi tallafin iraruwa da kayan noma da takin zamani”, a bayyana.

Idan dai ba a manta ba, sama da mutum miliyan daya ne ta dalilin wannan rikici na Boko Haram

suka bar gonakin su da gidajen su. Yayin da a yan kwanakin nan sama da mutum 5,000 sun koma

a muhallan su da nufin ci gaba da gudanar da rayuwar su kamar yadda suka saba. Kuma wannan ci gaban ya samu ne tadalilin qoqari da qwarin gwiwar jami’an tsaro wajen taimakawa jama’ar.

Hukumar FAO ta himmatu wajen yiwa matsalar aikin gona da samar da abinci kan-da-garki, ko a matsayin warware tarnaqin da ka iya dabai-baye manoma dangane da aikin nasu, musamman ‘yan gudun hijira. Saboda haka, wannan bangare ne na shirin farfado da al’ummar yankin arewa maso-gabas dagwamnatin tarayyar Nijeriya ta sa gaba domin bunqasa yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here