Dalilin Da Yasa Zainab Boni Haruna Zata Ci Zabenta A Jihar Yobe

1
606
Madam Zainab Boni

Daga Hussaini Muhammad Baba, Fika

Zainab Boni Haruna, matar tsohon gomnan jihar Adamawa ta fito takaran kujeran Majalisan tarayya na kasa a karkashin Jam’iyar PDP.

Zainab ta gana da manema labaru jim kadan bayan ta kaddamar da yakin neman zabenta a garin Gadaka.

Tayi wannan Alwashin ne lokacin da taga dandazon magoya bayan ta wanda sukazo wajen taronta da Tayi. Kuma dubban mutane ne suka halarci taron inda kusan kashi 70 na mutanen mazaban suka halarci taron.

‘Na tabbata cewa zan samu nasara a wannan zaben da za’ayi lura da yadda na samu karbuwa a yankin namu. Mutanen yankin sun kuma kara jadda damin cewa zasu zabi jam’iyyar PDP a zaben da yake gabatowa”.

Madam Boni ta kuma kara da cewa zan mazabarta sunsha wahala dama da shekara 27 saboda wakilai da suke samu Wanda basuda kishinsu.

Kwamitin yakin Neman zabe na sun jima suna shiga lungu-lungu, sako-sako dan tambayan matsololin da mutanen mazabar suke fama dashi.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here