Da Hikmah Ake Mulki, inji  Dr Sheriff Almuhajir

0
670
Hon. Mala Buni

Sakamakon an baiwa Farfesa takarar gomnan jihar Borno sai wasu mutane ke damun mu da cece-ku-ce akan cewa dan takarar mu na Yobe baiyi zurfin karatu ba, saboda haka suke gani bai cancanta ba. Wannan rubutun baya nufin cewa Farfesan Borno bashi damar hikmar mulki ba ne, ba kuma kalubalantar shi ake nufi ba, ana bayanine akan cewa babban dolene sai ka zama Farfesa zaka iya mulki ba.

Farko dai ya kamata mu fahimci cewa ilimi daban hilkmah daban, a gudanar da mulki Hikmah ake bukata ba zunzurutun ilimi ba, hikmar adalci, kyautatawa, juriya, tausayi da fahimtar madafin iko da iyakokin su.

Shi yasa Allah ta’ala yake banbanta Hikmah da ilimi da yake cewa “يعلمهم الكتاب والحكمة” wato Allah na baiwa Annabawa martaba ta ilimi Sannan yayi basu Hikmah. Suna karantar da ilimi na takarda wanda kuma suna koyon hikmah ta rayuwa. A wani wajen yace “يؤتي الحكمة من يشاء ومن يؤت الحكمة فقد أوتي خيرا كثيرا

Yace yana zaben wanda yake baiwa hikmah cikin mutane, kuma dukkan wanda Allah a bashi Hikmah, to lallai ya bashi alheri Mai yawa.

Sannan idan muka duba tarihin Annabi Sulaiman da Annabi Dawud. Duk da cewa Allah ya fifita Annabi Dawud a ilimi, harma ya aikoshi da zabura, amma Allah ya baiwa Annabi Sulaiman hikmar mulki fiye da shi. Misali lokacin da makiyaya biyu suka kawo kara wajen Annabi Dawud, sai yayi hukuncin da Allah ke gani ba daidai bane, sai Allah ya baiwa Annabi Sulaiman hikmah kuma ya warware hukunci mahaifin shi Annabi Dawud shi. Har Allah ke cewa

( وداود وسليمان إذ يحكمان في الحرث إذ نفشت فيه غنم القوم وكنا لحكمهم شاهدين . ففهمناها سليمان وكلا آتينا حكما وعلما وسخرنا مع داود الجبال يسبحن والطير وكنا فاعلين

Anan Allah ya tabbatar da tarin ilimine ke tabbatar da kwarewa akan mulki ba, domin gabatar Annabi Dawud da ilimi amma ma’kerine ba”a bashi mulkin mutane ba, amma dan shi Annabi Sulaiman sai aka bashi Mulkin mutane, Aljanu, da ma tsuntsaye da sauran dabbobi.

Sai mu dawo kan Farfesa, shin wanene Farfesa, Farfesa shine wani da ya mallaki degree na uku wato PhD Sannan yayi taro kwarewa a wani fanni guda na ilimi. Farfesa mai ilimi ne, amma ko a tsangayar shi bai isa yace ya san komai ba,  sannan ko shine ya shigo mulki dole sai yayi komishinoni da mashawarta, wannan yana tabbatar da cewa wadanda basu kaishi zurfin karatu ba ne za su nuna mashi abunda zai yi, wannan ya nuna ba Farfesancin shi bane zai gudanar da gomnati.

Ilimi abune mai darajar gaske, amma bashi ke tabbatar da kwarewa a mulki ba, sau nawa aka baiwa Farfesa da PhD mulki amma suka jefa al-ummmah cikin garari. Mu duba jamioin mu da ke hanun Farfesoshi, shin sun tsira ne daga ta’annuti da sauran laifukan da ake yi a ma’aikatun gomnati? Jonathan ai PhD ne shin yafi Yaradua, ko Buhari kwarewa?

Ya kamata mu gane cewa Allah ne ke bada mulki ga wanda yaso kuma baya la’akari da irin abunda muke laakari da su wajen fifita bayin shi. Idan Allah ya baiwa mutum mulki to insha Allah zai bashi damar aiwatarwa sai dai Idan yaki bi, kamar yadda yake cewa

لا يكلف الله نفسا إلا وسعها

Daga karshe ina shaidawa masu fatan Alheri cewa Dan takarar mu Alhaji Mai Mala Buni mutumne mai saurare, da jin shawara da muhimmancinta ilimi da masu ilimi, kuma insha Allah zai iya kokarin shi wajen aiki da shawarar su domin tafiyar da ingatacciyar hukumah. Masu kokarin kaskantar da shi kuma suyi hakuri da ikon Allah mu hadu mu tayashi adduah Allah ya bashi hikmah ya kara mashi tsoron shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here