Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Matasan Jihar Yobe daga Komared Usman bn Affan

0
771
Usman bn Affan
Yana daga cikin abubuwan da a kullum ke mayar damu baya ta fuskar cigaba, rashin hadin kai sakamakon rashin fahimta da mutunta ra’ayin juna. Wannan matsala ta dade tana wargaza tsakanin Matasan mu a matakai daban-daban, Kuma har ya zuwa wannan lokaci mun kasa samun bakin zaren warware irin wadannan matsaloli.
A fahimta ta, kuskure ne mu kalubalenci ‘yan uwanmu Matasa dake gwagwarmaya, saboda sun shiga harkar siyasa tsundum. A tunani irin nawa, wannan riga Malam masallaci ne, domin bamu basu jarabawar da suka kasa cin nasara akai ba. Bai kamata a ko yaushe, mu munanta zato ga mutane ba tare da fahimtar manufar su ba musamman a al-amari na siyasar da muka dade muna korafin rashin damawar mu ciki ba.
Idan ma kalubalantar su zamu yi, to kamata yayi mu jira idan ALLAH yasa sun shiga gwamnati, kuma suka yi watsi da lamuran Matasa sabanin yadda suka nuna zasu yi yanzu, babu laifi mu fito mu kalubalen ce su saboda amfani da sunan Matasa wajen neman wurin shiga.
Kullum muna ihu tare da zargin rashin damawa damu cikin harkokin siyasa dama gudanarwar gwamnati a dukkan matakai, shin muna zaune ne kawai za’a kira mu a dama da mu ba tare da mun bayar da wata gudumawa ba, musamman wajen tabbatar da nasarar gwamnatin? A’a, hakan da kamar wuya. Shige fagen daga a daidai wannan lokaci, shine tinkahon mu, kana shine makamin da zamu ke amfani wajen jefa fargaba ga wadanda muke zargi da rashin bamu damar, saboda a matsayin mu na wadanda muka bada gudumawa, muna da bakin maganar da za’a saurare mu idan gwamnati ta kafu. Muyi tunani.
Ya kamata mu kara tunani, domin rubuce-rubucen sukar gwamnati ba shine kawai mafita ba, saboda mun kwashe shekaru muna abu daya, har yanzu ba wani cigaban azo-a-gani da muka samar. Idan hagu taki, mai zai hana mu koma dama don gwada sa’ar mu? Saboda tabbatar da abubuwan da muke fatan Yobe ta riskesu ta fuskar cigaba. Kana zaune a gefe, ba zaka iya komai ba, dole sai kana ciki. Muyi tunani.
Dama kuma ba dole bane gabadaya ace ra’ayin mu yazo daya, amma bai kamata kullum mu fifita ra’ayin mu akan na wasu ba, yana da kyau mu mutunta ra’ayin kowa don tsare wa juna mutunci. Muna nan tare tun kafin siyasa, kuma da yardar ALLAH bambancin ra’ayin siyasa ba zai zama silar darewar mu gida-gida a matsayin ‘yan gwagwarmaya masu ra’ayin ganin cigaban Yobe ba.
Nasan galibi fargabar mutane shi ne, idan Matasan dake gwagwarmaya sun shiga gwamnati, to shikenan ba mai fadawa gwamnati gaskiya, ko kuma suyi tunanin cewa, tun dama gwagwarmayar ba don Talaka ake yi ba, illa don neman samun wuri. Gaskiya wannan kuskuren tunani da fahimta ne. Kuma ina mai tabbatar muku cewa, shigar Masata cikin tafiyar siyasar nan ne kadai hanyar da zai baiwa ‘yan gwagwarmayar saukin isar da koke-koken al-umma dama fadawa gwamnati gaskiyar daya kamata ta sani don amfanar talakawa da yardar ALLAH.
Muna da labaran Matasa da dama a wasu sassan duniya da suka rike manyan mukamai na siyasa, wadanda idan mun tuna dasu suke bamu sha’awa, shin mun taba tambayar kanmu yadda suka tsinci kansu a wadannan matsayin da suke bamu sha’awar har muke alfahari dasu? Kodai a tunaninmu kawai suna zaune ne akace suzo ga matsayi? Wannan bazai taba yiwuwa ba ga duk wanda yayi nazari, dole sai da suka yi wata sadaukarwa ta hanyar bayar da gudumawa a lokacin da ake bukata. Muyi tunani.
Wadannan Matasa da wasunmu ke zargi a halin yanzu da bin wasu ‘yan siyasa koma jam’iya, bafa hanaka gudanar da naka al-amarin siyasar sukayi ba, kuma don kayi naka ra’ayin ba zai zama kayi laifi a wurin su ba. Domim abin da na fahimta, wasu suna korafi ne saboda Dan takarar da wadannan mutane ke marawa baya baiyi musu ba saboda wasu dalilan su, domin kila suma da wani dan takarar da suke so sabanin wannan. Wanda dashi aka marawa baya, ba zasuyi korafi ba. Babu wanda zai hanaka goyan bayan duk wanda kake ga ya cancanta musamman idan kana da dalilai da suka tabbatar da cancantar sa kamar yadda wadancan suke da nasu dalilan cancantar wanda suka bi.
Wani abu da ya kamata mu fahimta kuma shine, wadannan Matasa da wasu keta cece-kuce kansu, samuwar su cikin gwamnati babbar dama ce a garemu wajen isar da koken talakawan mu. Sannan, wata dama ce har ila yau a garemu na samun damar cika burinmu na shiga domin a dama damu a harkokin siyasa da gwamnati da a kullum muke ihun cewa ba’a bamu sakamakon rashin damawa damu.
Ba ta yadda zasu dama damu matukar bamu dama dasu yanzu ba. Ina nufin yanzu da suke neman goyon baya dama kuri’unmu. Muyi tunani.
Yau idan akace wani daga cikin Matasa na cikin gwamnati, bamu da haufi wajen tunkararsa kan bukatun talakawa, musamman idan yanzu mun karfafa masu gwiwa tare da basa cikakkiyar goyon baya da ya kamata. Amma ta yaya zaka fuskanci mutumin da yanzu kake ta kalubalanta saboda munanta masa zato akan yadda ya shiga siyasa, idan ya samu dama a cikin siyasar? A gaskiya, ga mai kunya irina, da kamar wuya ya iya tunkarar sa koda kuwa don Talaka zai je badon kansa ba. Wannan misali ne.
Har ila yau, cikin abubuwa da nake so mu sake tunani akai shi ne, babu Matashi d’aya da har yanzu muka ji labarin ya siya fom na takarar Gomna balle muyi tunanin mara masa baya. Don haka nema wasu daga cikinmu suka bi inda suke tunanin zai biyawa ‘yan uwansu Matasa bukata, hakan ya zama laifi kenan duk da ‘yancin hakan da doka ta basu damar yi? Muyi tunani.
Muyi hakuri mu kai zuciya nesa, ako da yaushe mu daina munantawa junanmu zato saboda banbancin ra’ayi musamman na siyasa. Idan muna tunanin rashin daidai akan wani mataki da wasu suka dauka daga cikin mu, babu laifi mu tuntubesu don jin karin bayani dama kila fahimtar da juna baki daya kan yadda zamu bullo tare da tunkarar al-amarin. Wannan shine cigaba ba kananan maganganu ba. Muyi tunani.
Comr Adams Oshomhole, Sen Shehu Sani da ire-iren su, nasan sun sha gabanmu wajen abinda ake kira Gwagwarmaya, amma da suka tabbatar burinsu na gwagwarmayar bazai cika ba, har sai sun shiga fagen siyasa, sun shiga kuma muna ganin abubuwan da suke yi, idan sun tsaya kananan maganganu zasu kai inda suke yanzu? Wannan shine tunanin daukar wasunmu suka yi, har suka dauki matakin da suka dauka yanzu. Kuma idan basu yi yanzu ba, yaushe muke so suyi? Yaushe za’a fara damawa damu? Yaushe zamu bada gudumawar mu? Ko kawai mu cigaba da kallo muna surutai a shafukan sada zumunta? Muyi tunani.
Wannan ra’ayina ne, kuma nayi ne don farkar damu saboda mu fuskanci zahiri. Kada mu cigaba da yaudarar kanmu. Ga duk wanda yaga kuskure a cikin wannan rubutun nawa, babu laifi ya ja hankali na don mu gyara tare, banyi dan wata manufa ba sai don bayyana fahimta ta kan abinda nake ga ya yafi dacewa damu.
Kuma ina bamu shawarar yin komai da niyya mai kyau, domin niyyamu itace ribarmu a wurin ALLAH. Kada duniya ta rudar damu, mu mance lahira. ALLAH ya sa mu dace.
Usman Bin-affan Damaturu
08038001563

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here