“Babu laifi idan aka baiwa sarakuna madafu a kundin tsarin mulkin kasar nan”-Inji mai martaba sarkin Potiskum

0
378
Mai martaba sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mai martaba sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya bayyana cewa “bayar da madafa (constitutional role) a sarakunan gargajiya a kundin tsarin mulkin kasa, wasu suna ganin hakan bazai yi kyau a sarakuna ba, saboda zasu shiga harkar siyasa”.

Mai martaban ya fadi haka ne a yayinda wakilan gidajen jaridu na jihar Yobe suka je yi masa ta’aziyyar rasuwar Wazirin Potiskum, Alhaji Muhammadu Guza.

A yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida game da wannan furucin nasa, yace “to idan ka duba irin gagarumar gudunmuwar da sarakuna suke bayarwa a cikin al’umma, wannan din ni a gani na bazai kawo illa a zaman sarauta ba, saboda an bashi madafa a kundin tsarin mulkin kasar nan.”

Mai martaba sarki ya cigaba da cewa “ko a yanzu sarakuna suna da madafu, wanda gwamnati ta basu, tun a ranar da aka nada ka, za a baka wasu abubuwa wanda zaka kula da su, kamar kula da al’adun jama’a, kula da sha’anin addini, kula da wasu abubuwa da zasu shafi mutanen ka. Abin da za a bawa basarake, baza a bashi matsayi na shari’ah ba, baza a bashi matsayi na yin doka ba, baza a bashi wani matsayi na hukunta wani abu na ‘executives’ ba. Akwai madafu (roles) da za a basu, kuma wannan madafu bazai wuce na jagorancin al’umma ba, saboda haka wannan din ya nuna kamar sarakuna ba a ma basu aminci na rawar da zasu taka a kasa ba, to amma idan aka basu wani matsayi, wanda zasu iya takawa a cikin kasa, to wannan din zai basu karfin gwiwa, akan cewa, kasa tayi na’am da irin taimako da suke bayarwa, kuma ta amince da matsayin sarakuna, cewa, suna daya daga cikin mutanen da za a iya komawa a tafi dasu kuma a amince da wasu abubuwa da suke yi.”

Sarkin na Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, ya kara da cewa “amma a yanzu a tsarin mulkin kasar nan basarake yana iya kokarin sa ne, a ce shugaban jama’a ne kawai, to anan idan wani abu ya taso bashi da wani madafa a kundin tsarin mulkin kasar nan, saboda haka ni a gani na, ko da an bayar da karfin cewa, basarake a bashi madafa a kundin tsarin mulkin kasar nan, babu laifi, don kuwa ina iya tunawa a kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1979, a ciki ance, a bawa sarakuna kashi biyar cikin 100 na kudin da za a kawo, to in har a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan, yace a bawa sarakuna kashi biyar bisa dari, na kudin da za a kawo, to yaya kuma baza a bashi dama ko madafa da zai aiwatar ba? Ka bawa mutum kudi, kace yayi aiki, baka kuma bashi inda zaiyi aikin ba. Saboda haka ni ina ganin a gargajiyance, mu ‘yan Afirka da kuma ‘yan Nijeriya, basarake in an bashi madafa a kundin tsarin mulkin kasar nan, zai yi abin da ake bukata, saboda haka ni banga laifin a baiwa sarakuna madafu a kundin tsarin mulkin kasar nan ba.”

Mai martaba tare da wakilan jaridu a fadarsa. A hagun sa akwai Mohammed Abubakar, shugaban ‘yan jarida wakilai kuma ma’aikacin Daily Independant,a hagunsa akwai Ibrahim El-tafsir, wakilin Neptune Hausa sannan a daman mai martaba kuma Malam Ahmad ne, mawallafin mujallar Jakadiya sannan sai Babayo Wakili, wani gawurtaccen dan jarida, kuma malamin ‘yan jaridu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here