Aske Gashin Samari A Potiskum: Abinda Doka Yace Daga Barrister Gimba 

0
1068

Matasa dayawa sunyi kuka a cikin garin Potiskum saboda aski da ƴan sanda suka yi, a satin baya, a matasa dake barin gashi ko aske wani ɓangaren gashin kansu su bar wani ɓangaren. Yin kalan askin ana masa kallon baƙon al’ada ne da yake gurbatar da tarbiyar yara da kuma garin gaba ɗaya. Aske sa sai ya zama horo a masu shaye-shaye, zaman banza, da sauran su.

  1. 36(12) na Kundin Tsarin Milkin Najeriya na 1999 yace baza’a iya hukunta mutum akan laifin da ba’a rubutasa da hukuncinsa a cikin dokokin da majalisar ƙasa kota jiha tayi ba. Shi laifin da ake tuhumar matasa dashi bawai tara gashin bane, shaye-shaye, zaman kashe wando, da sauransu sai kuma ake yin amfani da gashi da kalar sa kayan da suke wajen kama mutane.

A S. 405(1) na Dokokin Hukunta Masu Laifi na Arewa, akwai laifin zama Idle Person, wanda baya aikata komai. Wannan irin mutum da zai iya kula da kansa da iyalensa amman yaƙi, duk wanda baida tsayayyen makwanci, aikin yi kuma bazai iya bada gamsarsiyar bayani akan shi waye bane. Duk me zuwa cha-cha bai kunyar jama’a, mai faɗace-faɗace da zage-zage acikin jama’a. Duk mai zagin kasuwa acikin jama’a ko ɗan ya bawa wani haushi da sauransu. Wannan anyi bayani akan irin matasan da Buhari yace basa tsinana komai wajen ci gaban ƙasan.

  1. 405(2) na Dokokin Hukunta Masu Laifi na Arewacin Najeriya yayi magana akan VAGABONDS, ya ƙunshi duk wanda an kama sa da laifin zama Idle person kuma ya sake yi, duk wanda aka kamasa da ƙarafun balla gida da niyan shiga gidan mutane, duk wanda ana zargin sa da sata kuma aka same sa yana yawo kusan shagon mutane da dare.

Akwai INCORRIGIBLE VAGABOND a S. 405(3) na wannan dokokin, shine mayawacin da baza’a iya gyara sa ba, kuma wanda an hukunta sa akan zama vagabond aka sake kamasa.

Hukuncin zama waɗannan shine:

  1. 406 — Idle Person: mai laifi bazai wuce wata uku a gidan yali ba, ko kuma a ci taron sa, ko kuma a tura sa gidan yari kuma aci taronsa.
  2. 407 – Vagabond: Hukuncin shine za’a rufe mutum har zuwa shekara guda, ko kuma aci taronsa ko a rufe sa kuma aci taronsa.
  3. 408 – Incorrigible vagabond: Za’a rufesa a gidan yari zuwa shekara biyu, ko aci taronsa ko kuma a kulle sa ya kuma bada taron.
  4. 409 – A wajen gamsarwa cewa mutum yayi niyan aikata laifin, ba sai an nuna cewa ya aikata wannan laifin ba. Za’ayi la’akari da yadda abubuwa suka gudana da kuma halin mutumin.

Ance kuma a mutanen da akayi wa aski akwai ƴan shaye-shaye, S. 403 na Dokokin Hukunta Masu Laifi na cewa duk wani musulmi da yasha abin sa maye wanda ba ɗan magani bane, hukuncinsa shine za’a kullesa a gidan yari har zuwa wata ɗaya, ko kuma aci taronsa Naira goma ko a kullesa kuma aci taronsa. Darajan kuɗin mu ya faɗi, saboda haka taron zaifi haka.

Daga bisa abinda muka gane akan laifukan nan, tara gashi bai ɗaya daga cikin hanyoyin nuna cewa an aikata wannan laifukan. Saboda haka in an kama mutum ya kamata wasu dalilai daban ne suka sa bawai gashin sa ba.

Acikin case na Theresa Onwo V. Nwafor Oko (1996) 6 NWLR pt 456 p. 612, wata mata ne mijinta ya mutu yabarta sai ƴan uwansa suka kamata suka mata askin dole bisa al’adansu, kotu ta yanke cewan an taɓa mata right to personal liberty nata. Shine dama da kowane ɗan ƙasa yake da a ƙarƙashin S. 35(1) na Kundun Tsarin Mulkin Najeriya nayin duk abinda yaga dama in dai ba laifi bane. Za’a iya ƙiransa “ƴan cin kai”

Shi wannan daman da aka bawa ɗan ƙasa bai aiki idan kotu tazo yanke wa mutum hukunci, in yaƙi yin abinda wajibi ne a kansa, kawo sa gaban kotu da zargin ya aikata laifi, yaro me ƙasa da shekaru sha takwas dan saboda ilmantar dashi ko domin kula dashi, mutu mai rasar lafiya irinsu ebola da zai shafi mutane, mahaukata ko masu taɓin hankali, wanda sun shahara a shaye-shaye saboda gyara su da kuma kare mutanen gari.

Duk wanda ƴan sanda suka kama sa, yana da daman ƙin faɗa musu komai, yaƙi amsa tambaya har sai yaga lawyan da yake wakiltan sa. S. 35(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Duk wanda aka kama yana da ƴancin a gaya masa, a rubutance kuma a yaren da yasani, laifin da ake tuhumar sa dashi. S. 35(3) na Kundin Tsarin Mulki

Duk wanda aka kama, yana da ƴan cin a kawosa gaban kotu a cikin gaggawa dan kar a tauye masa hakkinsa. S. 35(4) na Kundin Tsarin Mulki

A yanzu mun gane abubuwa kaman haka:

1) Ƴan sanda nada daman kama masu laifi da arubuce yake kamar shaye-shaye, zaman banza, sata, da sauransu.

2) Kotu kaɗai ke iya hukunta masu laifi, dan haka askin da aka mawa yara bai kamata ba.

3) Ya kamata da ƴan sanda su kai su gaban kotu akan laifin da ake tuhumar su dashi.

4) In kotu ta kama su da laifi zata yanke masu hukunci daidan laifinsu.

5) Ƙarban kuɗin aski da akayi awajen yara da kuma naira ɗaribiyar bai kamata ba, saboda gwamnati ke hukunta mutum kuma gwamnati ke ɗaukar nauyin hukunta su da gyara su, shiyasa ƴan gidan yari ke samun komai kyauta. Wannan kuma bawai ya bawa ƴan sanda matsayin hukunta mutane bane.

SHAWARA DA ZAN BADA wannan shawaran a matsayina na mai son ganin ci gaban garin ne, bawai doka bane… Na gama faɗan dokokin a baya.

1) Yara sune manyan gobe, in har tarbiyarsu ta lalace, kenan babu maganan ci gaba kuma a garin. Saboda baza su girma su zama abin koyi ana ƙasa dasu ba.

2) Abinda ƴan sanda suka yi, duk da doka bai basu dama ba, ana ƙiransa A NIP IN THE BUD, a rufe matsala tun yana ƙarami kafin yayi jijiyoyin da zasu maƙale acikin ƙasa, a gagara gyara sa.

Saboda inda ƴan sanda sun kai matasan nan kotu, za’a rufe su tare da manyan masu laifi ne kafin a fara shara’a. Yin hakan zai sa yara su ɗauko wasu halayen da yafi ƙarfin su.

In an yi shara’a, aka gama sa aka samu mutumin bai aikata laifin nan ba zai dawo gida amman duk da haka dole ne ya ɗibo wasu ɗabi’u a gidan yari… Kuma ba lalle bane agama case in da wuri.

In kuma an samu mutum da laifi, to zaman sa a gidan yari zai kai a ƙalla wata ɗaya zuwa shekara biyu.

Yin askin kamar anma mutum horo ne dan yayi tunanin abinda zai iya faruwa dashi in yaci gaba da bin hanya marar kyau.

3) Ya kamata Ƙaramar Hukumar Potiskum ta haɗa kai da ƙungiyoyin matasa dan saboda ana sanar da matasa duk abinda bai dace ayi ba.

Za’ana yin haka ne awajen Public Lectures, manyan makarantu, asibitoci da wajen tara jama’a.

4) Ya kamata ana tura hukuma wajaje kamar sabuwa tasha, Yobe line da sauran wajaje da ana zargin ana saida miyagun ƙwayoyi ana kama masu sayar wa. Wannan aiki NDLEA ne, in har  hukumar garin ta haɗa kai dasu to zamu cimma burin mu.

5) Bayan kowa ya gyara kuskurensa, sai a yafe wa juna. A ɗau komai tamkar be faru ba, saboda komai na duniya mai wucewa ne kuma watarana sai labari.

Barrister Gimba shine Coordinator na Forward Yobe, Forward (FYF) zaka iya tura masa saƙo a 08100000888 ko slimanigeezer@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here