An tsinci gawar jaririya akan juji a garin Potiskum

0
2517
Gawar jaririyar da aka tsinta a Potiskum

Daga Yahaya Wakili, Potiskum

Abin al’ajabi kuma abin tausayi, yayinda jiya da safe da misalin karfe sha daya aka tsinci gawan jaririya mace a kan juji da ke bayan Unity Bank a garin Potiskum a jihar Yobe.

A lokacin da wakilin Neptune Hausa ya ziyarci wajen, wani mutum mai suna Alhaji Bala yace yana wucewa daga wajen da misalin karfe sha daya na safe sai wadansu yara dake tsince–tsince a kan jujin suka sanar da shi cewa ga wata jaririya a cikin tsumma.
Alhaji Bala yaci gaba da cewa a lokacin da ya iso wajen sai ya ga gawan jaririya mace a cikin tsumma wanda daga halamu haifuwan asubahi ce. Daga nan sai shima ya shaidawa wadansu mutane masu wucewa, nan da nan sai jama’a suka taru ana ta alhini dangane da abin da ya faru.

Ya ce yana tsammani matar, ko budurwar tazo daga wata unguwa ne tayi wannan aika-aikan.

Daga nan sai yayi kira ga iyaye dasu rika sa ido akan ‘ya’yansu musamman yara mata domin barin ‘ya’ya mata balagaggu kara zube shike kawo irin wadannan abubuwan.

Shima, wani malamin Qur’ani, mai suna Alhaji Yunusa Muhammad yace aikata irin wadan nan abubuwan Àllah (SWT) ya kan saukar da bala’i da masifu kala-kala ga bayinsa,daga nan sai yayi kira ga jama’a da su rika tarbiyar da ‘ya’yansu akan koyarwan manzon Àllah sallallahu alaih wa sallam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here