Amina Bashir: Farfesa mace ta farko daga Yobe

0
621
Fassara daga Hussaini Mohammed Baba
Farfesa Amina Abubakar Bashir ta zama farsesa a Shekara ta 2009,  an haifeta 8th June 1960 a garin Potiskum, Yobe State, amma kuma ita yar Daya ce, Fika  Local Government.
Ta fara makarantanta daga central primary school Nguru, lokacin tana kuruciyanta Alhaji Garba Daya, Hakimin Daya kuma shine Mai-anguwan daya da kuma Galadiman Fika sannan kuma shi Mai hada maganin gargajiya ne a garinsu.
Ta cigaba da makarantanta na farko a S.T Patrick (Makarantan Mishan ne) kuma shine makaranta mafi kyau a Maiduguri a lokacin, yayinda babanta aka sanja mishi wajen aiki zuwa babban birnin da aka kirkiro a lokacin na arewa maso gabanshin kasan.
Bada dadewa ba, babanta aka kara sanja masa wajen aiki, ita kuma ta gama makarantanta na farko a Dambua dake Potiskum, bayan wannan makarantan sai ta samu takardan izinin karatu zuwa Government Girls College Maiduguri, ta gama a 1977.
Ta fito daga zuri’an da sukasan darajan ilimi, bata samu daman zama a gida ba, ta wuce kolejin gwaninta na kimiyya dake mubi a cikin Adamawa State. Daga bisani ta samu wani takardan zuwa makarantan nazari na asali a cikin jami’an Ahmadu Bello dake Zariya.
Ta fara aikinta a 1982, nandanan ta wuce bautan kasanta a matsayin mataimakin mai degree na biyu a cikin Jami’an Maiduguri, lokacin tayi aiki sosai saboda tana bukatar tattara abubuwan da zata zama farfesa. Ta tafi tabar aiki zuwa Jami’an Dutse dake Jigawa State. Lokacin data tsaya a matsayin mataimakin shugaban makaranta ta bangaren ilimi.
Farfesa Bashir tana kaiwa ziyarar aiki a makarantu da dama a Nigeria kuma tanada bazawa sama da hamsin harda wallafa takardu da sunanta na shugaban tsangayan ilimi na gwaninta a Jami’an dutse.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here