Amaryar honarabul, mai dimple da kyaun diri, ta arce bayan ta lashe naira miliyan 30

1
4527
Honarabul da Amaryarsa mai dimple

Daga Hussaini Mohammed Baba

Mai neman takarar gwamnan jihar Jigawa a jam’iyyar PDP Hussaini Namadi Auyo ya kai karar amaryarsa da mai dalilin aurenta bisa laifin guduwa daga gidansa bayan kashe naira miliyan 30 wurin aurenta.

Hussaini Namadi wanda tsohon dan majalisar tarayya ne mai wakiltar Hadejia/Auyo/Kafin Hausa a jihar Jigawa ya shigar da karar ne a kotun shari’ar Musulunci dake Shahuci, Kano.

Lauyan Namadi, Ukashatu Adamu ya shaidawa kotu cewa honorabul ya bada kwangila ne a samo masa mata a jamhuriyar Nijar “Fara,doguwa, mai dogon gashi, mai wushirya, mai dimple, dara-daran idanuwa, da kyaun diri.”

Ukashatu Adamu ya shaidawa kotu cewa bayan an dace da samo amarya mai suna Jamila, dawainiyar bikin da hada-hadar jigilarta da danginta daga Nijar zuwa Nigeria ta lashe fiye da naira miliyan 30.

Sai dai makonni uku da tarewar Jamila sai ta nemi ta ziyarci gida, inda daga can ne ta ce ba zata dawo ba sai dai honarabul ya sake ta.

Dangane da haka ne Hussaini Namadi ke neman ko dai kotu ta tilasta a dawo masa da matarsa ko kuma ta karbo masa kudinsa naira miliyan 30.

A nasa bangare, lauyan dake kare amarya da mai dalilin aure, Sa’idu Tudun Wada ya bukaci kotu ta cire mai dalili daga cikin shari’ar kasancewar ta sauke nauyin da aka dora mata na samo amaryar da ta cika sharuddan da Hussaini Namadi  ya lissafa.

Sai dai alkalin kotun, Garba Ahmed ya ki amincewa da wannan bukata.

Dagan nan kuma lauyan ya bukaci a basu dama su sulhunta da juna, inda ya yi wa Hussaini Namadi tayin auren kanwar Jamila tun da dai ita ma “fara ce, doguwa, mai dimple” har ma ta fi yayar kyaun diri.

Yanzu haka dai alkali Garba Ahmed  ya dage cigaba da sauraron karar zuwa 15 ga watan Maris, 2018.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here